Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta dawoda karɓar harajin motoci da ke zirga-zirga a manyan titunan ƙasar.

Ministan ayyuka da gidaje a Najeriya Babatunde Fshola ne ya sanar da haka a yau Laraba bayan majalisar zartarwa a ƙasar ta amince da dawo da harajin.
Ministan ya ce an ɗauki matakin dawo da karɓar harajin ne domin faɗaɗa hanyoyin samar da kuɗin shiga a ƙasar.

Minsitan ya ce tun tuni akwai tsarin biyan harajin wanda a halin yanzu za a dawo da shi.

Tsarin harajin wwanda ake biya sama da shekaru 15 sai dai an dakatar da karɓar sa amma a wanna lokaci za a dawo da shi.
Tsarin harajin zai bai wa ƙananan motoci damar biyan naira 200 sai kuma manyan motoci da za su dinga biyan naira 500.
Karɓar harajin ba zai shafi motocin jami’an tsaro ko babura da kekuna ba, haka kuma bai shafi motocin gwamnati da ma’aikatu ba.