Mutane 146 ne su ka mutu a sakamkon annombar cutar amai da gudawa da ta ɓarke a jihar Kebbi.

Gwamnatin jihar ce ta bayyana haka wadda ta ce mutane 2,208 ne su ka kamu da cutar a faɗi jihar baki ɗaya.
Babban likita a asibiti Sir Yahaya Memorial wanda ya ke a Birnin Kebbi Dakta Aminu Halliru Bunza ne ya sanar da haka.

Ya ce cutar ta fallatsa a ƙananan hukumomi 20 na jihar.

Ya ce a halin yanzu gwamnatin jiharna yin duk mai yuwuwa don ganin an dakatar da yaɗuwar cutar a fadin jihar.
A makon da muke ciki ne dai gwamnatintarayya ta bayyana cewar cutar amai da gudawa ta halaka sama da mutane 800 a ƙasar.
Sai dai masana na alaƙanta hakan da yawaitar ambaliyar ruwan sama da ake fama da shi a bana.