Hukumar zaɓe mai zaman kan ta a Najeriya INEC ta yi gargaɗi a kan wani shafi ba boge da aka bude da sunan ta.

Hukumar ta ce an bude wani shafin Intanet ne da sunan shafin da ta ke yi wa mutane rijistar kafin zabe na din-din-din.
Kwamishinan zaɓe a Najeriya kuma shugaban kwamitin wayar da kai a kan al’amuran katin zabe Festus Okoye ne sa sanar da haka a wata sanarwa da ya sanya wa hannu.

Ya ce hukumar ba ta sahalewa kowanne kamfani ko ma’aikata don yin rijistar katin zabe ba, haka kuma bas u da alaƙa a akan shafin da a ka buɗe da suna ta don yin rijistar zabe ga ƴan Najeriya.

Hukumar ta nesanta kan ta daga dukkan wani kamfani ko ma’aikata da ke yin rijistar da suna ta sannan ta nesanta kan ta daga shafin da aka buɗe mai suna REGISTER.INEC.PVC.ONLINE.
Sannan ta ce shafin intanet da ta ware don karɓar bayanan yan ƙasar don yin rijistar zabe shi ne CVR.INECNIGERIA.ORG.
Hukumar ta ce a na ci gaba da yin rijistar katin zaɓe a ofishin hukumar na jihohi da ƙanana hukumomi a faɗin Najeriya.