An kashe mutane huɗu da sace ɗalibai 15 bayan da su ka fi awanni biyu su na ɓarin wuta a makaranatar

Aƙalla mutane huɗu a ka kashe yayin da a ka tafi da ɗalibai da malamai a dare Lahadi wayewar yau Litinin.

Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun kai hari kwalejin aikin noma da ke Bakura a jihar Zamfara tare da sace ɗalibai.

An sace ɗalibai 15 da malami sai matar malamin da ƴayan su biyu.

Ƴan bindigan sun buɗe wuta a yayin da su ka kai harin sannan su ka tafi da ɗalibai da malamin da iyalan sa.

Haka kuma ƴan bindigan sunkashe mutane hudu waɗanda ake zargin jami’an tsaro ne ciki har da ƴan sanda.

A ɓangaren ƴan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin tare da bai wa jami’an su umarnin ceto su cikin gaggawa.

A wata sanarwa da kakakin yan sandna jihar ya fitar a safiyar yau, ya ce kwamishinan yan sandna jihar ta shirya wani zaman gaggawa da hukumomi a makarantar don jin bahari tare da ɗaukar mataki na gaba.

Jihar Zamfara na fama da hare-haren yan bindiga wadanda ke sace mutane tare da halaka wasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: