Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da shugabannin tsaron Najeriya a ranar Alhamis.

Wannan ne taro na farko da shugaban zai yi bayan dawowar sa daga birnin Landan.
A watan sanarwa da aka fitar sanarwar ta ce, shugaban zia gana da shuganannin tsaron ne don lalubo hanyar da za a magance matsalar tsaro da ake fuskanta a ciki.

Sanarwar ta ƙasa da cewar jami’an tsaron ƙasar sun jajirce a kan aikin su wanda hakan ke tilastawa yan bindiga da mayaƙan Boko Haram su ke miƙa wuya.

Ganawar za ta bayar da dama don sanar da shugaban ƙasar halin da ake ciki a kan tsaron ƙasar da kuma irin ci gaban da aka samu tun bayan tafiyarsa Landa.
Shugaba Buhari ya ziyarci birnin Landan wanda ya dawo a ƙarshen makon a ya gabata.
Shugaban ya killace kan sa don cika sharudan dokar Korona bayan mutum ya dawo daga tafiya.
Zai fara da bikin sanya hannu a kan dokar man fetur ta PIB wadda ya saya wa hannu a jiya Litinin.