Aƙalla ɗalibai goma yan bindiga su ka sace a Sakkai da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Daga cikin mutanen da aka sace akwai malami guda a cikin su.
Kakakin yan sandan jihar SP Gambo Isah ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ƴan bindigan sun sace ɗaliban ne a ranar Talata.

A wani labarin kuma ƴan bindiga sun kashe mutane 11 a Ɗansadau da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Hare-haren na zuwa ne bayan yan bindiga sun kama wasu ɗalibai da malamai a wata kwaleji a Zamfara sannan su ka nemi kudin fansa naira miliyan 350.
Satar ɗalibai a arewacin Najeriya ya zama ruwan dare ganin yadda da dama daga cikin jihohin arewacin ƙasar a ke sace ɗaliban.
An fara da sace ɗaliban makaranatar sakandiren mata ta Chibok a jihar Borno wanda mayaan Boko Haram su ka yi shekarun da su ka gabata.