Babbar kotun jihar Kano ƙarƙshin mai shari’a Aisha Ibrahim Mahmod ta yankewa wani Nura Gwamda hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yankewa Nra Gwanda hkuncin ne bayan an tabbatar ya aikata kisan kai.

Kotun ta samu Nura Gwanda mai shekaru 35 a duniya wanda ya kashe wani Mudan Ibrahim wanda ke da shekaru 27 a duniya.

Nura Gwnada ya aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 2018 a unguwar Fagge a Kano.

Al’amarin ya fara ne yayin da Nura ya je wajen mamacin don karɓar naira dubu uku wadda ɗan uwansa ya ara masa kuma wannan ne yay i silar samun saɓani a tsakanin su lamarin da ya kai ga aikata kisan.

Nura yay i amfani da wuƙa wajen daɓa wa mamacin a ciki da kuma baya, yayin da ƴan sanda su ka ɗauki wanda aka cakawa wuƙar zuwa babban asibitin kwararru na Murtala likitoci sun tabbatar d acewar ya rasu.

Laifin da ake zargin sa da aikawa ya saba da sashe na 221 na kundin dokar da aka tanada a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: