Wasu ɓata gari sun rushe masallatai biyu a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.

Ɓata garin sun rushe masallatan ne taree da ƙone wasu shaguna 14 a wata kasuwa.

Jaridar Daily Nigeria ta ruwaito cewar shugaban wani bangare a kasuwar ya tabbatar mata da faruwar lamarin.

A ranar Laraba gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a ƙaramar hukumar Jos ta arewa.

Rikicin Jos na kwanan nan ya fara ne ƙasa da makonni uku yayin da wasu kirista su ka farwa musulmi matafiya sannan su ka yi musu kisan gilla.

Leave a Reply

%d bloggers like this: