Gwamnatin jihar Kano ta ce ta yi wa ɗaurarru 3,717 afuwa a cikin shekaru shida.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da haka y ace yay i hakan bisa amsa kiran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari don rage cunkoso a gidajen gyaran hali.

Gwamna Ganduje ya ce an yi wa mutanen afuwar ne daga shekarar 2015 zuwa shekara 2021 da mu ke ciki.

Bayanin ya fito ne yayin da tawagar wakilcin shugaban ƙasa a kan sauye-sauye da tsari a kan gidajen gyaran hali su ka kai wa gwamnan ziyara a ofishin sa ranar Alhamis.

Sanarwar da babban sakataren yada labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya fitar, y ace gwamna Ganduje ya yi tsarin yin afuwa ga ɗaurarru a yayin bukukuwan salla tun daga shekarar 2021 zuwa shekarar 2021.

Sannan a na biya wa mutanen da ake bi kuɗi sannan a bas u kuɗin da za su hau abin hawa zuwa gidajen su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: