Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara sun daƙile wani hari da yan bindiga su ka yi yunƙurin kai wa Shinkafi.

Ƴan bindigan masu yawa ɗauke da makamai sun nufi Shinkafi don kai hari ga jama’a sai dai ƴan sanda hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile harin.

Rundunar ta ce ƴan bindigan sungudu ɗauke da raunin harbi a jikin su sannan sun sami nasarar kashe guda daga cikin su.

A wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya fitar, y ace sun yi nasarar tarwatsa ƴan bindigan sannan wasu sun gudu ɗauke da raunin harbi a jikin su.

Kakakin ya ƙara da cewa, kwamishinan ƴan sandan jihar ya aike da jami’an tsaro masu yawa a garin don ganin an samar da ingantaccen tsaro.

A cewar sanarwar ƴan sanda ƴan bindigan sun fito ne daga sansanin babban ɗan bindiga da ake kira TURJI.

Kwamishinan yan sandan jihar ya umarci jami’an sa da su tabbatar sun samar da yanayi na tsaro don tsare lafiya da ratyuwar al’uma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: