Gwamnatin jihar Adamawa ta ta rufe wasu makarantun kwana guda talatin a sakakon fargabar tabarɓarewar al’amuran tsaro a jihar.

A wata sanarwa da kwamishiniyar Ilimi a jihar Wilbina Jackson ta fitar, ta c gwamnatin kulle makarantun ba tare da sanya wata rana don sake bude w aba.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne don tabbatar da tsare ɗaliban.

A na zargin gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne don kallon yadda ake sace ɗalibai a wasu jihohin arewacin Najeriya.

Gwamnatin ta ayyana wasu makarantu hudu da ta ce za su ci gaba da yin karatu a jihar.

Makarantun sun hada da ƙaramar makarantar sakandiren mata ta Yola, sai makarantar kwalejin General Murtala Muhammed Yola da Special School Jada sannan Special School Mubi.

ɗaliban da ke sauran makarantu 30 da gwamnatin ta rufe za su dinga zuwa makarantun je ka dawo a makarantu mafi kusa da su.

Gwamnatin ta buƙaci hukumomi a ɓangaren da su rungumi matakin da ta ɗauka don tabbatar da tsare rayuwar ɗaliban.C

Leave a Reply

%d bloggers like this: