Labarai
Ƴan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro Tare Da Ɓalle Gidan Yari A Kogi
Rahotanni daga jihar Kogi na nuni da cewar wasu yan bindiga sun kutsa tare da kai hari gidan gyran hali a jihar.
Ƴan bindigan sun shiga gidan gyaran halin ne a daren Lahadi wayewar Litinin sannan su ka yi silar kubutar da masu laifi a ciki.
Kafin shiga gidan gyaran halin sai da yan bindigan su ka kashe wasu sojoji da ke kan babbar hanyar Lokoja hanyar da ke kai wa zuwa gidan.
Masu laifi da ama ne su ka kuɓuta a gidan gyaran halin da ke Kabba a ƙaramar hukumar Bunu ta jihar.
Wasu daga cikin masu laifin da su ka gudu sun koma yayin da aka kama sama mutane 100 daga cikin wadanda su ka gudu.
Ba a bayyana adadin sojojin da aka kashe waɗanda su ke kan hanyar.
Ƴan bidniga sun fara kai hari gidan gyaran hali da ke jihar Imo wand aya yi sanadiyyar sama da masu lafi dubu su ka gudu.
Mai Magana da yawun hukumar gidan gyaran hali a jihar Enobore Frances ya tabbatar da hakan a yau, y ace aƙalla mutane 240 ne suka gudu a sakamakon harin.
Labarai
Mai Maganin Gargajiya Ya Harbi Kansa Bayan Yin Gajin Maganin Bindiga
Wani mai maganin gargajiya mai suna Ismail Usman ya harbi kansa a lokacin da yake gwajin maganin bindiga a yankin Kuchibiyi da ke Karamar Hukumar Bwari a birnin Abuja.
Wani mazaunin Kuchibiyi Samson Ayuba ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, a lokacin da mutumin ya ke kokarin gada ingancin maganin bindgar da ya hada.
Ya ce sai dai bayan faruwar lamarin an yi gaggawar kai shi asibitin gwamnati da ke Kubwa bayan ya fadi, inda kuma ya samu raunuka.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin na Abuja Joesephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ta fitar.
Adeh ta ce sun samu rahotan cewa wani mai maganin gargajiya ya harbe kansa a lokacin da yake gwajin maganin bindigar da ya hada.
Sai dai ta ce sakamakon munanan raunukan da ya samu aka kai shi asibitin Kubwa domin duba lafiyarsa, daga bisani kuma aka mayar da shi asibitin kwararru da ke Gwagwalada domin kara samun kulawa.
Kakakin ta kara da cewa abinciken da aka gudanar a gidansa an gano wata bindigar gargajiya da layu wadanda ya yi amfani da su gurin gwajin maganin bindigar.
Adeh ta ce a halin yanzu su na ci gaba da gudanar da bincike kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar makami ba bisa ka’ida ba tare da yunkurin hallaka kansa.
Labarai
Jami’an Soji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 100 A Sassan Najeriya A Mako Guda
Rundunar sojin Najeriya ta ce jami’anta sun samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda 135, tare da kama mutane 185 da ake zargi da aikata laifuka, da kuma ceto mutane 129 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na fadin Kasar nan a cikin mako guda.
Daraktan yada yada labaran hedkwatar tsaro ta Kasa Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan ne a yau Asabar a hedkwatar da ke Abuja.
Buba ya ce daga cikin wadanda aka kama ciki harda 61 da ake zargi da satar mai.
Acewar Buba ‘yan ta’adda a yankin Arewa ta tsakiya sun fara mika wuya ga sojojin su.
Labarai
Gwamnatin Kano Ta Mayarwa Da Jami’ar Yusuf Maitama Sule Asalin Sunanta
Gwamnatin Jihar Kano ta mayarwa da Jami’ar Yusuf Maitama Sule tsohon sunanta na asali.
Majalisar Zartarwar jihar ce ta dauki matakin mayarwa da Jami’ar tsohon sunanta, bayan wani taro da gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a jiya Juma’a.
Idan ba a manta ba dai a watan Yulin shekarar 2017 ne tsohon gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya canjawa jami’ar suna zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule, domin tunawa da marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule, bisa irin gudummawar da ya bai’wa Jihar, dama Kasa baki daya.
Sai dai kuma a halin yanzu gwamnatin Jihar mai ci karkashin Jam’iyyar NNPP ta dauki matakin dawowa da Jami’ar tsohon sunanta.
Northwest University ya samo asali ne a zamanin mulkun tsohon gwamnan Jihar Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya samar da ita.
-
Labarai10 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare6 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada6 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai6 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari6 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari