Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta kammala rijistar katin zaben mutane 931,768 a fadin ƙasar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Litinin ta ce ta yi aikin katin zaɓe da masu matsala har mutane 4,225,749.
A halin yanzu mutane 2,953,749 ne su ka yi rijistar katin zaɓe wanda aka fara fara tun a watan Yuni na shekarar da muke ciki.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce jinsin maza 2,308,338 ne su ka yi rijistar yayin da bangaren mata 1,917,411 su ka yi rijistar katin zabe.

Hukumar zaɓe INEC ta bude shafin yanar gizo don sauƙaƙa wa mutane hanyar rijistar katin zaɓe yayin da aka fara yin rijsitar da ɗaukar sauran bayanai a ofisoshin hukumar na ƙananan hukumomi a najeriya a watan Yuli.
A Najeriya akwai mutane kusan miliyan 200 sai dai ƙasa da mutane miliyan biyar ne su ka samu daman yin rijsitar katin zabe.