Rundunar sojin Najeriya ta ce mayaƙan Boko Haram na ɗaukar mutane aiki a jihar Borno.

Bayan dubban mayaƙan da su ka tuba tare da miƙa kansu ga jami’an tsaro, rundunar sojin ta ce a halin yanzu mayaƙan na aikin shigar da wasu mutane cikin ƙungiyar.
Mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Janar Onyem Nwachukwu ne ya bayyana haka a Maiduburi babban birnin jihar Borno yayin wani gangami a helkwatar dakarun rundunar Hadin Kai.

Kakakin ya ja hankalin mutane da su kula tare da sa ido a kan duk masu hulda da su a yankunan su.

Sannan ya ce rundunar na samun gagarumar nasara a kan yaƙi da take da yan ta’addan dasu ka addabi yankin gabashin ƙasar.
A baya rundunar ta ce ta karɓi mayaƙan Boko Haram sama da dubu biyar waɗanda su ka tuba tare da miƙa makamansu ga jami’an tsaro.
A halin yanzu rundunar na yin duk mai yuwuwa wajen ganin ta bi tsarin da yadace wanda aka samar da doƙar ƙasa da ƙasa a kan mayaƙan.