Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da rufe gudanar da rijistar katin zaɓe da ta ke ci gaba da yi a wannan lokaci.

Hukumar ta ce ta cimma kaso na farko bisa hudu na tsarin gudanar da ci gaba da rijistar katin zaɓen a wannan karon.

A wata sanarwa da kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan al’uma a kan katin zaɓe Festus Okoye ya fitar, ya ce an dakatar da yin rijistar daga yau yayin da za a sake bude shafin a ranar 4 ga watan Okotoba mai kamawa wanda za a kammala kashi na biyun ranar 20 ga watan Disamba.

Mutanen da hukumar ta yi wa rijistar katin zaɓen a halin yanzu sun haira miliyan uku yayin da ake ci gaba da kammala wa.

Daga cikin waɗanda su ka yi akwai wadanda su ka yi sabuwar rijistar da kuma waɗanda su ka yi gyara da da masu buƙata ta musamman da sauran rukunin al’umma maza da mata.

A ranar 28 ga watan Yuni hukumar ta bude wani shafin yanar gizo don sauƙaƙa wa mutane yadda za su mallaki katin zaɓen nasu a ko ina su ke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: