Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya ce Najeriya ta na goyon bayan samar da tsari da dokokin a kan yaduwar makamai a yankin Afrika.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin babban tarin majalisar dinkin duniya karo na 76 wanda ya gudana a binrinin Newyork.
Shugaban da ya yi jawabin sa a ranar Juma’a ya ce Najeriya ta na samun nasara a kan yaki da mayaƙan Boko Haram da kuma sauran ƴan ta’addan da su ka addabi ƙasar.

Ya ƙara da cewar Najeriya da sauran ƙasashen Afrika na goyon bayan samar da tsari da dokokin da za su taimaka wajen yaɗuwar makamai a yankin domin daƙile ta’addanci a yankin Afrika.

Taron da aka gudanar wanda aka yi masa take da Gina jajircewa ta hanyar kyakkyawan fata don murmurewa daga annobar Korona.
Haka kuma Najeriya za ta marawa majalisar dinkin duniya don ganin an magance matsalar sauyin yanayi.
Shugaba Buhari ya ce akwai rashin kyakkyawan shigabanci musannan wanda ke kan turbar dimokaradiyya wanda kana ke sa ana take haƙƙin ɗan adam.
Shugabanni sama da 80 ne su ka halatrci taron majalisar dinkin duniya a bana.
Shugaban Najeriya ya gana da mutanen da su ka yi rakiyar sa zuwa Amuruka bayan ya halarci taron.