Kotun Shari’r musulunci da ke Ƙofar Kudu a Kano ta ƙi amincewa da buƙatar lauyoyin Sheik Abduljabbar Kabara.

A zaman da kotun ta yi a yau Alhamis, sabbin lauyoyin Malamin sun buƙaci a bayar da belin sa domin iyalansa na cikin wani hali a dalilin rashin sa.
Buƙatar hakan na zuwa ne yayin da aka ci gaba da zaman shari’ar bayan lauyoyinsa na farko sun janye daga kare shi.

Lauyan da ya jagoranci lauyoyin kare Abduljabbar a yau ya buƙaci a bashi kwafin shari’ar tun kafin fara shari’ar.

Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Okotoba na gaba.
Gwamnatin Kano ce ta yi ƙarar Abduljabbar bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W da kuma yin kalaman da za su iya haddasa fitina a jihar.
Kafin gurfanar da shi a gaban kotu, malamin ya bukaci a shirya muƙabala tsakanin sa da malaman da ke ƙalubalantar sa amma ya gaza kare kalaman da ake tuhumarsa a kai.
Lauyoyin sa a yau sun ce matuƙar za a bayar da belin sa, malamin a shirye yake don yin bayanin da zai kare kansa a bisa tuhumar da ke yi a kan sa.