Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta nuna damuwa a kan yadda ƴan ta’addan IPOB ke kai hare-hare da nufin hana gudanar da zaɓe a jihar.

Hukumar ta ce ƴan ta’addan sun lalata kayan aikin ta masu muhimmanci sai dai ta maye gurbin su da wasu.

Hukumar ta gudanar da wani zaman gaggawa don duba hanyar da za a shawo kan matsalar ta’addancin yan ƙungoyar waɗanda ke kai hare-hare yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmod Yakubu ya ce sun fahimci cewar burin ƙungiyar shi ne hana zaben da ake dab da yi a jihar.

Sai dai hukumr ba ta karaya ba a kan yadda ƴan ƙungiyar ke kai hare-hare a jihar tare da saka dokoki.

A ranar Lahadi sai da ƴan ta’addan ƙungiyar IPOB su ka kai hari ofishin hukumar ƴan sandan farin kaya da ofishin hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura a Najeriya reshen jihar Anambara.

Ƴan ƙungiyar IPOB masu iƙirarin kafa ƙasar BIAFRA na kai harre hare ofishin hukumar zaɓe na ƙananan hukumomi tare da lalata kayan aikin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: