Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka ƴan bindiga da dama a hare-hare ta sama da su ka kai musu a maɓuyarsu da ke dazukan Katsina da Sokto.

Jaridar PRNigerira ta tabbatar da kashe yan bindiga 32 a dajin Rugu da ke iyaka da ƙaramar hukumar ƙanƙara ta jihar Katsina.

Ƴan bindigan da aka kaeh yaran wani babban ɗan bindiga ne da ake kira Gjere kuma an jikkata yaran nasa sama da 20.

Harin da sojojin su ka kai ya faru ne daga ranar 30 ga watan Satumba zuwa ranar 3 ga watan Okotoban da muke ciki.

Rundunar sojin ƙarƙashin shrin Hadarin Daji sun kai hare-hare kan maƙoyar ya bindigan ne bayan sun gano mabiyar tasu a cikin dajin.

Haka kuma an kashe yan bindiga da dama a dazukan da ke ƙaramar hukumar Sabon Birini da Isaa ta jihar Sokoto.

An kashe ƴan binidgan ta hanyar jefa bama-bamai a maƙoyar tasu wanda hakan ya bai wa sojojin nasarar kashe da yawa daga ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: