Rundunar yan sanda a Najeriya ta sanar da kama mutane 47 ciki har da mutane biyu da su ka sace ɗalibai a Kaduna.

An kama mutane biyu daga cikin waɗanda su ka sace ɗaliban makarantar Katolika ta Kaduna.
An kama mutanen da ake zargi da gaskuwa da mutane tare da kwato wasu makamai masu yawa daga hannun su.

Kakakin yan sandan Najeriya CP Frank Mba ya sannar da haka yau kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kan su.

Daga cikin makaman da aka kama akwai bindigu masu yawa da makami harbin jirgi da kumma harsashi sama da 500.
Frank Mba ya ce za a gurfanar da mutanen da ake zargi a gaban kotu da zarar yan sanda sun kammala bincike a kan su.
