Sufeton ƴan sandan Najeriya Usman Alƙali Baba ya tabbatar da samar da ƴan sanda na musamman domin tinkarar zaɓen gwamna a jihar Anambra.
Ya bayyana haka ne yayin ganawa da kwamandojin yan sandan kwantar da tarzoma a Abuja.
Ya ce ana bai wa dakarun wani horo na musamman yadda za su tafiyar da al’amuran zaɓe a jihar.
Alkali Baba ya ce za su tabbatar an gudanar da zaɓe ba tare da tayar da tarzoma ba.
Hukumar zabe ta sanar da gudanar da zaɓen a jihar Anambra duk da kai hare-hare da ƴan ta’addan IPOB ke kai wa muhimman wurare a jihar.