Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Kasafin Kuɗi Na 2022 Tsallake Karatun Farko

Majalisar dattawa da ta wakilai a Najeriya sun fara karatu na biyu a kan kasafin kudin shekarar 2022 na ƙasar.

Mako guda bayan gabatar wa majalisa kasafin wanda shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya yi, majalisar dattawa ta fara karatu na biyu a kan kasafin a ranar Laraba.

Kasafin ya tsallake karatun farko a zauren majalisar wakilan ƙasar a yau Alhamis.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 na naira Tiriliyan 16.39.

Daga cikin kasafin za a kammala manyan ayyukan da aka fara a ƙasar waɗanda ba a ƙarasa ba.

A na sa ran majalisar dattawa ta mayar da kasafin doka bayan kasafin ya tsallake karatu na uku a cikin shekarar da muke ciki.

Tun bayan gabatar da kasafin a zauren majalisar, shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawal ya tabbatar da cewar majalisar za ta tabbata ta kammala nazartar kasafin kafin ƙarshen shekarar 2021 tare da umartar kwamitin gudanar da harkokin kuɗi da tsare-tsare na majlisar ya fara gudanar da aikin sa cikin gaggawa.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: