Rundunar yan sandan jihar Gombe ta tabbatar da kama wani matashi mai shekaru 32 bisa zargin kashe mahaifin sa.

Al’amarin ya faru a ranar Asabar a ƙauyen Zange da ke ƙaramar hukumar Dukku ta jihar Gombe.
An kama Haruna Buba da zargin kashe mahaifinsa sakamakon kyautar wata babbar gona da ya bai wa yayansa.

Matashin ya hallaka mahaifin nasa ta hanyar saran sa da adda a kai bayan nuna ƙin amincewa da kyautar gonar da ya bai wa ɗan uwansa.

Bayan samun labarin haka, ƴan sanda sun kama wana ake zargi a wani gidan kallo da ke ƙauyen.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Mallum Buba ya tabbatar da faruwar hakan har ma ya ƙara da cewa za su gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan sun kammala bincike a kai.