Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban ciki har da fashi da makami da masu garkuwa da mutane.

Kakakin yan sandan jihar Ahmed Wakili ne ya shaida haka a wata sanarwa da ya fitar ranar juma’a.
daga cikin waɗanda aka kama akwai wasu mutane hudu Idi Abdulahi, Rabi’u Sulaiman Aliyu Malam da Hassan Baƙo da ake zargi sun kashe wani Jibril Aliyu a gidansa.
Ƴan sanda sun ce mutanen sun kashe mutumin ne ta hanyar harbin sa da bindiga.

Sannan an kama wani Idi Jibril da su ka hada baki su ka sace wani ɗa ga Ibrahim Dai tare da neman kudi fansa naira miliyan ɗaya da rabi.

Kakakin ya ƙara da cewa a ranar 4 ga watan Satumba an kama Nasir Gaddafi da Abdurrahman Mahmood sai wani Kabiru Saleh da su ka aikata fashi da makami a kuma su ka kashe wani Ɗanjuma Umar har lahira.
Ahmed Wakili ya ce su na ci gaba da gudanar da bincike a kan waɗanda aka kama kuma da zarar sun kammala za su miƙa su kotu don yanke musu hukunci.