Kwamitin da uwar jam’iyyar APC ta aike jihar Kano domin duba ƙorafi a kan zaɓen shugabancin jam’iyya ya kammala tattara bayanai a kai.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewar sun duba zaben da aka yi a filin wasa na Sani Abacha ne kaɗai tare da tabbatar da cewar babu wani ƙorafi a kan sa.

Kwamitin ya ce ya duba yadda aka gudanar da zaɓen sannan babu wani ƙorafi ko matsala da ta auku a yayin gudanar da zaben.

Sama da mako guda kenan aka gudanar da zaɓen shugaban jam’iyyar APC a matakin jiha, sai dai an samu wasu da su ka gudanar da nasu zaben a wani waje na daban.

ɓangaren da su ka yi zaɓe a filin wasa na Sani Abacha ya tabbatar da nasarar Albdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar da ya samu nasara.

Yayin da a ɓangare guda kuwa su ka ce Alhaji Ahmad Haruna Zago ne shugaban da su ka zaɓa a ciin jam’iyyar.

Wasu daga cikin sanatoci da ƴan majalisar tarayya sun keɓe tare da yin zaɓen nasu duka a rana guda.

Kwamitin da uwar jam’iyyar ta aike jihar Kano zai miƙa rahoton sa bayan ya koma babban birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: