Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin buɗew wasu kasuwannin mako-mako a jihar.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Ibrahim Dosara ya sanaywa hannu.
Gwamnatin ta bude kasuwannin ne bayan shafe fiye da watanni biyu da rufe su tare da ɗaukar wasu matakai don kawar da yan bindiga.

An buɗe kasuwannin Gusau, Nassarawar Burkullu, kasuwar Daji, kasuwar shinkafi, da kasuwar Ɗan Jibga.

Sai dai gwamnatin ta zayyana wasu dokoki na cin kasuwar bayan amince wa da bude su.
Daga cikin dokokin akwai haramta wa mutane shiga kasuwannin da bindiga da kuma yin barazana da sunan ƙungiya ko wata hukuma.
Gwamnatin jihar ta ce buɗe kasuwannin bai shafi bangaren dabbobi ba.
Gwamnatin Zamfara ta rufe kasuwannin mako-mako a jihar da kuma hana siyar da mai a jarka ko galar da taƙaita siyar da mai a ababen hawa don shawo kan matsalar tsaro.