Shugaban ya yi kira ga matasa da su dage wajen riƙo da sana’a domin dogaro da kan su ta yadda za su zamto dattijai na gari.

Shugaban kamfanin Mecca Medina Travel Agency Alhaji Bello Maiwada Abubakar ne ya yi wannan kira a yayin taron cika shekaru 5 da kafa Mujallar Matashiya tare da yaye ɗaibai da su ka koyi sana’o’i kyauta.

Ya ce ya na da kyau matasa su sake faɗaɗa tunanin su don ganin sun amfanar da waus mutanen ta hanyar koyar da su sana’o’in da su ka koya.

Alhaji Bello Maiwada ya ƙara da cewa matasa za su iya amfani da tunanin su wajen sauya tunanin sauran matasa da su ka ɗauki wata hanya ta daban domin ɗora su a kan hanyar koyoon sana’a domin smaar da ci gaba.

A yayin taron Mujallar Matashiya karrama wasu muhimman mutane waɗanda su ka bayar da gudunmawa ta fuska daban-daban.

Daga ciki waɗanda aka karama akwai shugaban hukumar zaɓe ta jihar Kano Farfesa Rikuwa Arabu Shehu, da Alhaji Bello Maiwada Abubakar, Alhaji Nura Sharif Liman, Malam Sani Yakubu, Aliyu Yusif, Alh Ado Muhammad, Alh Isma’il Abdullahi, Hon Ibrahim Rabi’u Tahir, Tahir Investment Sainadawo Film Production da iyalan marigayi Alhaji Aminu Adamu Abba Boss.

Guda cikin waɗanda aka karrama Nura Sharif Liman ya yi jan hankali ga matasa bayan kammala taron.

Wannan shi en karo na hudu da Mujallar Matashiya ta yaye ɗalibai da su ka koyi sana’o’in dogaro da kai.

An yaye ɗalibai 47 sai waɗanda aka bai wa horo a kan aikin jarida mutane 19.

Daga cikin sana’o’in akwai ɗaukar hoto mai motsi da hoto mara motsi kula da ingancin hoto, gyaran janareta da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: