Kamfanin mai a Najeriya NNPC ya ce kada ƴan ƙasar su matsa wajen siyan man fetur domin su na da shi a ƙasa kuma wadatacce.

Mai magana da yawun kamfanin Barba Muhammad ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

Ya ce kamfanin ya na da mai da ya haura lita biliyan 1.7 a ƙasa.

Ya ce kada ƴan Najeriya su firgita a kan ƙarancin sa da ake yaɗa wa cewar babu wanda hakan ya sa wasu daga cikin gidajen mai su ke rufe wa.

Sannan ya ƙara da cewa baya ga man da su ke da shi a ƙasa su na tsammanin shigowa man fetur da yawa a cikin makonni da watanni a nan gaba don hana yankewarsa.

Kamfanin ya ce ba shi da wata masaniya a kan yunƙurin gwamnati na ƙara farashin man fetur a nan kusa.

Sanarwar ta ce kada ƴan ƙasar su matsa wajen siyan man fiye da buƙatar su a kullum domin babu wata alama na yankewar sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: