Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi kasar Afrika ta Kudu bayan ya kammala ziyarar aiki a ƙasar Faransa.

Mai magana da yawunsa Femi Adesina ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar yau Asabar.

Ya ce shugaban ya wuce kasar Afrika Ta Kudu ne daga birnin Paris domin halartar wani taro da za a fara daga 15 ga watan da mu ke ciki zuwa 21 ga watan da mu ke ciki.

Taron da za a yi a Afrika ta Kudu bankin kasuwanci na Afrika ne ya shirya haɗin gwiwa da hukumar ƙasashen Afrika ta AUC.

A wannan tsakani dai shugaban ya ziyarci ƙasashe uku bayan dawowarsa daga ƙasar saudiyya ya ziyarci ƙasar  Burtaniya sannan ya je ƙasar Faransa yayin da daga can ya wuce izuwa ƙasar Afrika Ta Kudu.

Shugaba Buhari ya ziyarci ƙasar Faransa taron zaman lafiya bayan da shugaban ƙasar Emmanuel Macron ya gayyace shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: