Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da kashe wasu mutane 15 a jihar sakamakon harin ƴan bindiga.

Tambuwal wanda ya bayyana haka jim kaɗan bayan gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 a zauren majalisar jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Litinin wanda ya ce mutanen da aka kashe na cikin ƙananan hukumomin Illela da Goronyo.

An kashe mutanen ne a yayin wasu hare-hare da aka kai ranar Lahadi da kuma safiyar yau Litinin a cewar gwamnan.

Ya ce an hallaka mutane 12 a Illela sai mutane uku da aka kashe a Gornyo, sannan akwai wasu da dama da su ka jikkata a sanadin hare-haren.

Sannan ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mutanen da su ka mutu a ƙayukan da ke ƙananan hukumomi biyu na jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: