Hukumar Hisbah a jihar Kano tya kama wasu mata 11 yayin bikin zaɓen sarauniyar kyau a jihar.

Babban darakta a hukumar Ustaz Aliyu Musa ne ya bayyana haka yau bayan sumamen da su ka kai.
An kama ƴan matan 11 da namiji guda wanda shi ya shirya taron.

Hukumar ta ce ta kama matasan tare da kwalaben barasa da dama a yayin taron.

An kai sumamen filin shaƙatawa na NITEL trainig center da ke kan tintin Katsina a Kano.
Daranktan ya ce za su ci gaba da kai sumame dukkanin wuraren da ake zargin maza da mata na fakewa tare da aikata badala a jihar.
Sanarwar ta mai magana da yawun hukumar Lawal Ibrahim Fagge ya aike wa Mujallar Matashiya, daraktan ya ce hukumar za ta tabbatar da ana bin dokoki kamar yadda Allah ya tsara.