Ƴan sanda a jihar Jigawa sun kama wasu mutane goma a bisa zargin aikata laifuka daban-daban a jihar.

An kama mutanen ne a ƙananan hukumomin Taura da Kiyawa.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wasu da aka kama su da barasa ta gargajiya da ake kira Burkutu.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Lawa Shiisu ya tabbatar da cewar akwai wasu mutane uku da aka kama su a ƙauyyen Gujungu da Kwalam da ke ƙaramar hukumar Taura.

Sannan an kwato kayana maye masu yawa daga ciki akwai sholisho da wasu kaya da ake zargi mutanen sun sata.
Sauran mutane bakwai kuwa an kama su a ƙauyen Shuwarin da ke ƙaramar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.
Tuni aka fra bincike a kan masu laifin waɗanda za a gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala binciken.
A ranar 9 ga watan Okotoba ƴan sanda a Jigawa sun kama mutane 14 da ake zargi da aikata laifuka a ƙananan hukumomin Kazaure da Gumel.