Sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ne ya sanar da haka a yau Asabar.

Wannan wani mataki ne da gwamnatin ta ɗauka don ganin ta kawo ƙarshen ta’addancin sace-sacen mutane da neman kuɗin fansa.
Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ne ya bayar da umarnin hakan nan take.

Gwamnatin ta zayyano wasu babura da ke cikin dokar da aka hana siyar da su akwai Bajaj, Boxer, Qiujeng, Honda ACE, Jingchen, da sauran babura da ƙarfin su ya kai 185.

Haka kuma gwamnatin ta jaddada dokar hana ɗaukar fasinja a babur maiƙafa biyu a babban birnin jihar da sauran garejin gyaran baburan.
Gwamnatin ta jaddada dokar hana hawa babur daga ƙarfe 6:00 na yamma zw=uwa ƙarfe 6:00 na safe.