Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura a Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja ta ce mutane 156 ne su ka mutu a sanadiyyar hatsari a Abuja.

Kwamandan hukumar a Abuja Oga Ochi ne ya shaida hakan ranar Asabar bayan sun tattara alkaluman a kan mutanen da su ka rasu sanadiyyar hatsari a Abuja.
Ya ce akwai mutane 1,572 da su ka sami rani daban-daban a sanadin hatsari a Abuja.

Ƙididdigar da su ka fitar ta fara ne daga watan Janairun shekarar 2021 zuwa watan Nuwamban da mu ke ciki.

Kwamandan ya ce haɗɗuran sun faru ne a sanadiyyar rashin bin dokokin hanya kamar yadda doka ta tanada.
Daga cikin dokokin da aka fi karya wa akwai gudun wuce sa’a wanda ya haifar da aukuwar haɗɗura da dama a Abuja.
Ƙididdigar ta nuna cewar an samu haɗɗuran mota a Abuja guda 850.