Shugaban kamfanin mai a Najeriya NNPC Mele Kyari ya ce akwai yuwuwar farashin litar mai ya ɗaga zuwa 340 a shekara mai zuwa.

Hakan ya biyo bayan aniyar da gwamnatin shugaba Buhari ta saka a gaba na janye tallafin man fetur a kasar.

Farashin litar man fetur a Najeriya na iya kai 320 zuwa 340 a cewar shugaban kamfanin mai.

Tuni gwamnonin kasar su ka shirya goyon bayan janye tallafin man a ƙasar.

Asusun bayar da lamuni a duniya ya bukaci shugaban Najeriya Buhari ya gaggauta janye tallafin man fetur da na lamtarki zuwa sabuwar shekara mai zuwa.

Wannan dai alama cee da ke nuni daa karin farashin wutar lantarki da ta man fetur a Najeriya nan daa shekarar 2022.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: