Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Buhari Na Ganawa Da Manyan Tsaron Najeriya A Abuja

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro a Najeriya yau Alhamis.

An gabatar da taron don duba halin da ƙasar ke ciki na matsalolin tsaro musamman da ake fuskanta a halin yanzu.

Hakan ya biyo bayan sabbin hare-hare da yan bindiga ke kai wa hanyar Kaduna zuwa Abuja tare da sace mutane da dama.

Daga cikin waɗanda su ka halarci taron na yau akwai mataimakin shugaban NajeriyaFarfesa Yemi Osinbajo, mai bai wa shugaban ƙasa shawara a kan harkokin tsaro da babban harsan sojin Najeriya.

Sannan akwais hugabannin sojin saman Najeriya da shugaban sojin ruwa sai hugaban sojn ƙasa sannan sufeton ƴan sanda na ƙasa.

Taron ya mayar da hakali ne a kan nasarorin da aka samu a fannin tsaro a Najeriya a ƴan kwanakin nan.

A yayin taron na yau shugaba Buhari ya ƙara wa babban dogarin sa girma daga laftanal zuwa muƙamin Kanal.

Najeriya na fuskantar barazanar tsaro tsawon lokaci tare da ci gaba da faɗaɗa a sauran jihohi.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: