Hukumomin lafiya a Najeriya sun ce su na kan kulawa don gano ko akwai mai ɗauke da sabon nau’in Korona mai haɗari a ƙasar.

Hukumar lafiya a Najeriya haɗin gwiwa da hukumar daƙile cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ce ta ce su na ci gaba da bincike tare da bibiya don samo bayanai ko akwai mai ɗauke da cutar.

Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da hukumomin su ka fitar a yau Litinin bayan an gano wasu yan Najeriya masu ɗauke da cutar nau’in Omincron a ƙasar Canada.

Hukumar NCDC ta ce har yanzu ba ta samu bayanai a kan masu ɗauke da cutar ko wanda sabon nau’in cutar ya halaka a kasar ba.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ce ta sanar da samun sabon nau’in cutar wanda ta ce ya na da matuƙar haɗarin da ya fi sauran nau’in cutukan baya.

Hukumomin sun ce su na ci gaba da aiki tukuru domin rage yaɗuwar cutar Korona tare da tabbatar da bin dokokin ta a Najeriya.

Sannan sun buƙaci ƴan ƙasar su ci gaba da bin dokokin da za su taimaka wajen hana yaduwar cutar Korona domin hana yaɗuwar ta.

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewar zuwa ƙarshen shekarar 2022 za a kawo ƙarshen cutar Korona baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: