Rundunar sojin saman Najeriya ta yi nasarar lalata kayan yakin mayaƙan Boko Haram a jihar Borno.

Rundunar ta ce ta tarwatsa mayaƙan da ke Gajiram tare da ƙwato wasu makamai daga hannun su.

Sojojin sun ce harin da su ka kai haɗin gwiwa ne tsakanin dakarun sojin ƙasan ƙasar da sojojin sama Najeeriya.

Bayan kai harin an gano wasu gawarwaki da ake zargin na mayaƙan Boko Haram ne guda 26 a wurin da aka kai harin.

Rundunar ta ce yayin fafatawa da mayaƙan ta rasa jami’antsa guda biyu.

An kai wa mayaƙan harin ne yayin da su ka shiga garin kuma daga cikin kayan yaƙin da aka lalata nasu akwai igwa da sauran makamai.

Rundunar sojin ta ce ta yi amfani da sabon jirgin yakin da aka siyo na Tucano wajen kai hari a kan mayaƙan.

An siyo jirgin tare da kawo shi Najeriya domin yaƙi da yan bindigaa da su ka daɗe su na addabar ƙasar musamman ma yankin arewaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: