A safiyar Asabar ɗin nan wasu mayakan Boko Haram sun tashi abin fashe unguwar gida dubu ta jihar Borno.

Wasu mutanen mazauna wata unguwa da ke makwaftaka da filin sauka da tashin jiragen sama sun tashi cikin ruɗanin sakamakon fashewar wani bam a unguwar.

Hakan na zuwa ne bayan an hallaka wasu jami’an soji bayan mayaƙan Boko Haram sun kai  hari sansanin sojin a Rann ƙaramar hukumar Kala Balge a jihar.

Wasu hotuna sun nuna yadda bam  ɗin ya tarwatsa wani gida da ke cikin unguwar.

Sai dai hukumomi ba su bayyana aadin mutanen da su ka mutu a sakamakon harin da aka kai yau Asabar ba.

A makon da mu ke gab da bankwana da shi ne wasu mayaƙan Boko Haram su ka sace wasu matafiya 15 a wata hanya a Borno.

Kafin hakan kuma wasu rahotanni sun ce an sace wasu ma’aikatan gwamnati a jihar Borno kuma har yanzu babu wani bayani a dangane da abin da ake ciki don sakin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: