Minsitan tsaro a Najeriya Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya ya gargaɗi jami’an soji da su ƙaurace wa dukkan wani abu da ya alaƙantu da siyasa.

Bashin Magashi ya yi wannan gargaɗi ne yayin babban taron shekara shekara da aka saba yi na rundunar sojin Najeriya.
An gudanar da taron na shekarar 2021 a yau a Abuja.

Minsitan ya hori jami’an sojin da su mayar da hankali wajen aikin da ke wuyan su tare da kawar da dukkanin wata hanya ta ɗaukar ɓangaranci ko ssiyasa a cikin aikinsu.

Bashir Magashi mai ritaya ya ce aikin soja na da tsari wanda ya ke a cikin kundin tsarin mulkin ƙasa kuma bin tsarin sa shi ke tabbatar da gudanar da aikin da ƙwarewa.
Sannan ya ƙara jaddada gargaɗi ga jami’an wajen ganin sun kauce wa dukkanin wani al’amari na ɗaukar ɓangarancin siyasa wanda hakan ya saɓa da dokar aikin sojan Najeriya.
Sannan ya yaba wa babban hafsan sojin Najeriya a bisa ƙoƙarin sa wajen ganin ya gudanar da aikin da aka ɗora masa.