An samu ƙarancin lantarkin ne sakamakon yajin aikin da ma’aikatan su ka tsunduma ranar Litinin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin korar hukumomi a kamfanin raraba hasken lantarki na Abuja.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun ƙaramin ministan lantarki Ofem Uket ya sanya wa hannu a yau.

Korar ma’aikatan ya biyo bayan yajin aiki sa aka shiga wanda ya yi silar samun ƙarancin wutar a Abuja, Nassarawa, Kogi da jihar Neja.

Ƙungiyar ma’aikatan rarraba wutar sun tsunduma yajin aikin ne sanadin rashin biyansu wasu haƙƙoƙinsu da su ka ce gwamnati ta ƙi basu.

Tuni shugaba Buhari ya bayar da umarnin saka sabbin shugabanni a manyan muƙamai na hukumar.

Ƙungiyar ta fara yajin aikin ne a ranar Litinin lamarin da ya sa aka samu ƙarancin wutar lantarki a jihohin.

Sai dai gwamnatin ta ce ta yi zaman sulhu da masu ruwa da tsaki a kan batun a baya sai dai ba a cimma matsaya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: