Aƙalla ƴan bindiga uku aka cafke a maɓoyarsu da ke yankin Ossra-Irekpeni yayin da mafarauta su ka yi musu kwanton ɓauna.
An kama ƴan bindigan da ke ɓoye a dajin babbar hanyar Lokoja-Abuja.
Mafarautan sun shoga yankin ne a ranar Laraba bayan amun bayanai a kan ƴan bindigan da ke ɓoye a dajin.
Kafin kama ƴan bindigan sai da aka yi musayar wuta a tsakaninsu.
Wani daga cikin mafarautan ya shaida cewar da dama daga cikin ƴan bindigan sun gudu ɗauke da ranin harbin bindiga a jikinsu.
Daga cikin ƴan bindigan da aka kama sun yi bayani a kan yadda su ke mallakar makamai da kuma sauran mutanen da su ke hulɗa da su.
Shugaban ƙaramar hukuma Adavi ya tabbatar da faruwar lamarin.
Waɗanda aka kama na daga cikin ƴan bindigan da su ka addabi babbar hanyar Okene-Lokoja-Abuja.