Rundunar sojin Najeriya ta fatattaki ƴan b indiga yayin da su ka kai hari nSabon Tasha a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.

Sojojin sun yi hanzarin zuwa wajen bayan da ƴan bindiga su ka je a daren Juma’a wayewar yau Asabar.
Ƴan bindigan sun banka wuta a wani gida bayan da su ka gaza tafiya da mai gidan a unguwar.

Jami’an sojin sun ci ƙarfin ƴan bindigan al’amarin da ya sa su ka gdu ba tare da cimma nasara a kan harin da su ka shirya kai wa ba.

An ɗauki tsawon awanni ana musayar wuta da yan bindigan kafin jami’an su fatattake su.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewar taimakon jami’an sojin bayan an kira su ne ya sa ƴan bindigan su ka gaza gudanar da abin da su ka tsara.
Jami’an staron sun yi hanzarin zuwa wurin da abin ya faru a kan lokaci bayan da su ka karɓi kiran waya daga mutanen yankin.
Sai dai yan sanda ba su magantu a kan lamarin ba, bayan da mu ka tuntuɓi kakakin ƴan sandan jihar Muhammad Jalige ba mu samu damar yin magana da shi ba.