Wata babbar kotun jihar Jigawa da ke zaune a Kazaure ta yanke wa wani mutum mai shekaru 70 a duniya hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun sa da aikata fyaɗe.

Alƙaliyar kotun Justice Hussaina Adamu Aliyu ce ta karanto hukuncin yayin da kotun ta tabbatar da shaidun da su ke nuna mutum ya aikata laifin.
Mutumin ya aikata laifin ne a ranar 14 ga wtaan Oktoban shekarar 2020.

Haka kuma kotun ta yanke wa hukuncin a kan wani mai suna Murtala Idris ya aikata fyaɗen a kan wata ƙaramar yarinya mai shekaru 6 a duniya.

Mutanen da ake zargi sun musanta laifin da ake tuhumarsu da aikata wa.
Bayan gudanar da bincike tare da bibiyar shaidun da kotun ta samu ta gamsu da shaidar da su ka bayar sannan ta yanke wa waɗanda ake zargin hukuncinɗaurin rai da rai.
Tun tuni wasu jihohin ke ƙoƙarin samar da dokar kisa ko ɗaurin rai da rai ga mutanen da ake samu da laifin fyaɗe a jihohin su.