Hukumomi a ƙasar Koriya ta arewa sun sanar da haramta yin dariya da sauran abubuwan da za su nuna murna ga ƴan ƙasar tsawon kwanaki 11.

Matakin hakan na zuwa ne yayin da ake tunawa da ranar mutuwar tsoho shugabansu Kim Jong ll mahaifi ga Kim Jong Un shugaban ƙasar na yanzu.

Hukumomin ƙasar sun ɗauki matakin hakan ne domin nuna alhini ga mutuwar tsohon shugaban wanda ya mutu a shekarar 2011.

Tun a shekarar 2011ɗan marigayin Kim Jong Un ya karɓi ragamar mulkin ƙasar zuwa yanzu.

An haramta yin dariya da bukukuwa da sauran abubuwan da su ke nuna murna a ƙasar stawon kwanakin domin nuna alhini a kan rashin mahaifin shugaban.

Sannan an haramta shan barasa na tsawon lokacin da aka ƙayyade kamar yadda kakaki24 ta ruwaito.

Leave a Reply

%d bloggers like this: