Babbar kotun jihar Kano da ke zaune a Milla Road ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mai suna Balarabe Ahmad bayan ta same shi da aikata kisan kai a kan maƙocinsa.

Mai Shari’a Nasiru Saminu shi ya karanto hukuncin a zaman kotun na yau bayan gamsuwa da shaidun da aka gabatarwa kotun.
Ya ce hukuncin da aka yanke wa mutumin na ƙarƙashin sashe na 221 na kundin Penal Code.

Yayin gabatar da ƙararar an bayyana wa kotu cewar mutumin sun sami saɓani da maƙocinsa lamarin da ya kai ga ya caka masa wuƙa kuma silar da ta yi ƙarara kwanansa.

Sai dai wanda aka yanke wa hukuncin na da damar ɗaukaka ƙara zuwa kwanaki 30 zuwa kotu ta gaba.