Hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya Kwastam ta kama wata kwantena maƙare da sabbin bindigu da sauran makamai a Legas.

Hukumar ta kama motar ne a ranar juma’a bayan tsanananta bincike da hukumar ta yi a kai.
A bayanai da aka bayar an nuna cewar kwantenar na ɗauke da talabijin bango ta zamani wato Plasma sai dai bayan buda wa aka ga sabbin bindigu da sauran makamai a ciki.

Mai magana da yawun hukumar Uche Ejesieme ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce wata motar sintiri ce ta ta gano kwantenar maƙare da bindigu.

Tuni su ka ci gaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda su ke da kayan da kuma inda za a kai makaman.
Ya ce za su yi ƙarin bayani bayan sun kammala binciken su tare da samun cikakken bayanai a kan masu alhakin shigo da makaman.
Hukumar ta lashi takobin kama duk wani wanda ke da hannu cikin mallama ko shigo da makaman ba tare da ta saurara masa ba.