Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU za su yi zama na ƙarshe a yau don cimma matsaya kan tafiya yajin aiki.
Ƙungiyar ta yi wa gwamnati gargaɗi kafin zaman da za ta yi a yau.
Malaman jami’a a Najeriya na yunƙurin tafiya yajin aikin ne bayan an gaza cika musu burin su duk da sun gana da ɓangaren gwamnati a lokuta da dama.
Tafiya yajin aikin da malaman ke yi na kawo tsaiko a karatun ɗalibai a Najeriya.
Ƙungiyar na neman haƙƙoƙin ƴaƴan ta daga ɓangaren gwamnati wanda ta ce shekara da shekaru ba a biya su ba.