Rundunar ƴan sanda a jihar taraba ta yi nasarar kama wasu mutane 11 da ake zargin su da yin garkuwa da mutane.

Mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya CP Frank Mba ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce an kama mutanen ne a maƙoyarsu tare da ƙwato wasu makamai daga hannunsu.

Daga cikin makaman da aka kama a hannunsu akwai bindigu ƙirar AK47 guda bakwai, sai bindiga ƙirar Pistol guda biyu sannan harsashi da miyagun ƙwayoyi masu tarin yawa.

Ya ce mutanen da su ka kama na da alaƙa da hare-hare na kwanan nan da aka kai ciki har da kashe wani jami’in su guda ɗaya.

Ya ƙara da cewa ana zarginmutanen da sace hukumar hana fasa ƙwauri da kuma sace wani da ya ke da alaƙa da ɗan sarkin Jlingo.

Tuni aka ci gaba da bincike a kan mutanen da aka kama kuma za a ɗauki mataki na doka a kan su da zarar sun kammala binciken.

Leave a Reply

%d bloggers like this: