Mutane da dama ne su ka rasa rayukan su a sakamakon harin mayaƙan Boko Haram a jihar Borno.

Mayaƙan sun kai hari wasu ƙauyuka  a ƙaramar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno a ranar Lahadi tare da kashe mutane da dama.

A yayin da su ka kai harin sun ƙona gidaje da dama baya ga mutane da yawa da su ka kashe kuma har yanzu ba  kai ga gano adadin yawansu ba.

Wasu daga cikin mazauna garuruwan sun tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayuwarsu.

Sai dai an samu wasu da dama da su ka samu munanan raunuka a sanadiyyar harin mayaƙan Boko Haram.

Rahotanni na nuni da cewar jami’an tsaro sun isa garin bayan awanni biyu da ƴan bindiga su ka kai harin ƙauyukan.

Sama da shekaru 10 jihar Borno ke fuskantar rikicin mayaƙan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: